Menene Autism Spectrum Disorder

Autism:Itace cutar Galahanga wacce ake kira da Autism Spectrum Disorder (ASD) a turance. Autism: Cutar Galahanga ita aka sani da Autism a turance. Mustapha Safiyya, ɗaliba da ke karantar yadda jikin mutum yake gudanar da aiki (Human physiology) a jami'ar Ahmadu Bello davke Zariya. Ɗalibar ta gudanar da binciken a kan cutar Autism, kuma ta gabatar da maƙalarta a kan haka. Cutar Galahanga: Cuta ce da ke saka mutum rashin gudanar da mu'amala yadda ya kamata. Cutar Galahanga tana kawo rashin ƙwarewar sadarwa da matsaloli a cikin zamantakewa. Yaran da suke da wanna cuta suna fama da rashin sarrafa bayanai, sukan iya samun matsalolin koyo, an samo hakan sakamakon rashin daidaituwar na'urar sadarwa (neurodevelopmental disorder)a jikin mai fama da ita. Alamomin cutar Galahanga sun sha bambam ga masu cutar, amma hakan yana da alaƙa da matsalolin rashin fahimtar tunani, sadarwa, bacci da damuwa. Har a yau ba a san musabbabin cutar galahanga ba. Ɗalibar ta ƙara da cewa "sau da yawa ana kuskure wajen gane cutar baya ga rashin fahimta, amma bincike ya nuna faruwar hakan da ga neurobiological da muhalli". Ɗalibar ta ƙara cewa: "Galahanga tana faruwa ne a farkon shekarun yaro har izuwa karshen rayuwar sa. Babu magani kasidan ga cutar, amma fahimtar cutar ga iyaye da wuri yana ba da gudunmawa sosai wajen sanya farinciki mai ɗorewa ga masu cutar. Safiyya ta ja hankalin iyaye da cewa kada a bar mai cutar har a dunga cewa yanayinsa ne a haka ba cuta ba ce. Mungode da kulawa, ataimaka a tura saqon zuwa gurare daban-daban don a amfana

Comments

Popular posts from this blog

Kano State Indegenous Students of Tertiary Institution

NAFDAC Recruitments Portal

Rahotanni dangane da Hukumar kidayar jama'a ta kasa