Menene urinary tract infection (UTI)

 


Ko kasan Urinary track infection (UTI)?

Urinary tract infection (UTI): Itace cutar da ta shafi wani yanki acikin filin fitsari. Yankin ya hada da koda, mafitsara da urethra. Kimanin mutane miliyan 150 suna kamuwa cutar yoyon fitsari UTI a duk shekara goma, mafi yawancinsu mata ne. Idan cutar ta shafi mafitsara ana kiranta da cystitis a turance, idan tai tsamari tana shafar koda.Mafi yawan sanadin da cuta shine Escherichia coli, haka zalika kwayoyin cuta ko fungi na iya zama sanadi a wasu lokuta da dama. Abubuwa mafi hadari sun hada da ciwon sukari, jikin mace, jima'i, kiba ko tarihin iyali.

Alamomin cutar UTI

Cutar mafitsara tana haddasa jin zafi alokacin yin fitsari, yawan jin fitsari ko babu komai a mafitsasar. Game da ciwon koda kuwa, alamomin sun hada da ciwon baya, zazzabi, ciwon gabobi, jin zafin fitsari da jini. Masu cutar na fuskantar jin zafi a yayin fitsari ko kwanciya da iyali.

Magani

Magance cutar UTI shine maganin rigakafi wato antibiotic a turance da penicillin

Ana iya rarraba(sharing) wanan sako don anfanar mutane. Mungode.

Comments

Popular posts from this blog

HEMOGLOBIN

THE HEALTH BENEFITS OF MORINGA OLEIFERA

FROM THE TEA SELLER'S TABLE (DAGA TEBURIN MAI SHAYI)